Shiyyar Karaduwa: Yan takara 5 da ka iya zama barazana ga Sanata Abu Ibrahim a zaben 2019

Shiyyar Karaduwa: Yan takara 5 da ka iya zama barazana ga Sanata Abu Ibrahim a zaben 2019

Shiyyar Karaduwa: Yan takara 5 da ka iya zama barazana ga Sanata Abu Ibrahim a zaben 2019

0
0

A wani nazari da binciken da Katsina Post ta yi, dangane da masu neman kujerar dan majalissar dattawan Nijeriya mai wakiltar Katsina ta Kudu watau yankin Karaduwa, wadda Sanata Abu Ibrahim ke bisa kujerar yanzun haka a hawansa karo na hudu yana wakiltar shiyar a majalissar tarayya.

Haka ne wasu ke ganin yan shirya sun gaji da shi haka nan, suna bukatar wani sabon jini shima ya zo ya hau a ga irin tasa rawar.

Ta la’akari da haka a yanzun haka masu zawarcin jam’iyyar daga jam’iyyu daban-daban, da ake ganin kowannensu zai iya turzawa matuka wajen hambarar da Sanatan da yai ta yi ba canji a shiyar wato dai Abu Ibrahim.

Mutum na farko da aka fi ganinsa a matsayin babbar barazana ga Sanata Abu Ibrahim shi ne Shehu Inuwa Imam, wanda shi a jam’iyyar PDP yake shi kuma Abu Ibrahim yana jam’iyyar APC, to idan kowace jam’iyya ta tsayar da su takara, za su kara a tare, ana hasashen cewa Shehu Inuwa zai yi wuji-wuji da Sanata Abu Ibrahim a babban zabe mai zuwa na 2019.

Mutum na biyu da ake ganin, shi ma zai iya maye kujerar, ganin yadda matasan shiyar Karaduwa ke ta zawarcinsa da ya fito takarar sanatan shiyar Funtuan shi ne Arc. Kabir Ibrahim Faskari, wanda shi ma babban jigo ne a jam’iyyar APC a matakin tarayya da jihar Katsina, ana ganin yadda bai taba neman komai a jam’iyyar ba, a yanzun ya nuna yana so, zai iya samu ,ganin cewa yana daya daga cikin wadanda suka tsaya, tsayin daka wajen kafa gwamnatin APC a jihar Katsina dama kasa baki daya.

Mutum na uku kuwa da shi ma kalubale ga Sanata Abu Ibrahim shi ne Birgediya Janaral Maharazu Isma’il Tsiga mai murabus, wanda a kullum ba dare ba rana yana shiga cikin al’ummar Karaduwa lungu da sako, wajen yi masu jaje, ko barka, ko murna, tare da jin koken al’umma, ga shi ya gina matasa a shiyar wajen samar masu aikin hukumar NYSC a lokacin da yake a matsayin shugaban hukumar, a don haka ana ganin shima idan aka yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC zai iya barar da Abu Ibrahim.

Mutum na hudu da ake ganin shi ma abin tsoro ne ga Sanata Abu Ibrahim, shi ne Hon. Faruq Lawal Jobe, wanda babban makusanci ne ga gwamna Masari, masu hasashen siyasa na ganin, Jobe na iya doke Abu Ibrahim.

Sai mutum na biyar da ake hasashen shi ma yana bukatar kujerar Sanatan shiyar Funtua, shi ne Andaje daga karamar hukumar Malunfashi, sai dai shi ana ganin kusantaru da mahaifar gwamna mai ci za ta iya shafarsa don gudun kar a ce mulkin komai ya tare a yankin gari daya.

Baya ga wadannan yan takara 5 da muka yi bayaninsu a takaici, akwai wasu sauran yan takarar da za mu kawo maku nan gaba, wadanda suma babban kalubale ne ga Sanata Abu Ibrahim a shiyar ta Karaduwa, a babban zabe na 2019 dake ta kara tunkarowa.

To mi zai faru idan APC ta tsayar da Abu Ibrahim a matsayin dan takararta na sanatan shiyar Funtua a zabe mai zuwa? Abu na farko da bincikenmu ya hasaso shi ne jam’iyyar APC za ta iya faduwa a shiyar, saboda irin yadda wasu mutanen shiyar ke bayyana rashin gamsuwarsu karara da Abu Ibrahim ya ci gaba da wakiltarsu, ma’ana dai suna bukatar canji, su ga rawar da wani shima zai taka masu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *