Dalilin da ya sa matasan Karaduwa suka tsaida Arc. Kebram takarar Sanatan shiyar Funtua

Dalilin da ya sa matasan Karaduwa suka tsaida Arc. Kebram takarar Sanatan shiyar Funtua

Dalilin da ya sa matasan Karaduwa suka tsaida Arc. Kebram takarar Sanatan shiyar Funtua

0
0

A kwanakin baya wasu kungiyoyin matasa a shiyar Karaduwa sun aikowa Katsina Post da wasikar nuna goyon bayan su ga Arc. Kabir Ibrahim Faskari (Kebram), kwadayinsu a gare shi na ya amsa kiransu ya zama cikin zawarawan dake neman auren shiyar Karaduwa a babban zaben dake tafe na 2019, a cikin tutar jam’iyyar APC.

Matasan sun nuna gamsuwarsu, matuka dangane da yadda Arc. Kebram ke gudanar da lamuran da suka shafi rayuwarsa da kuma yadda yake hulda da jama’a wajen tsagye gaskiya komin dacinta, tare da tsare gaskiya da rikon amana a dukkanin huldodin da yake da jama’a.

Matasan sun nuna cewa muddin Karaduwa ta sami irin wannan gwarzon a matsayin wakilinta a majalissar dattawan Nijeriya, hakika shiyar za ta sami gagarumin ci gaba matuka, fiye da tunanin mai tunani.

Ko a kwanakin baya mun kawo maku labarin yadda wata kungiyar matasan shiyar Funtua gami da kungiyar Matasan Arewa suka karrama shi da lambar yabo, bisa kyakkyawan halayensa, da ita huldarsa da jama’a, da bikin ya gudana a cikin garin Funtua.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *