Alhamdulillah: Jirgin farko dauke da alhazan Katsina sama da 500 ya dawo gida

Alhamdulillah: Jirgin farko dauke da alhazan Katsina sama da 500 ya dawo gida

Daukar Nauyi: Rt. Hon. Abubakar Yahya Kusada

DAUKAR NAUYI: Hon. Salisu Yusuf Majigiri

Alhamdulillah: Jirgin farko dauke da alhazan Katsina sama da 500 ya dawo gida

0
0

Alhamdulillahi jirgin Alhazan jihar Katsina na farko dauke da Alhazai sama da dari biyar ya sauka lafiya a filin sauka da tashin jiragen na tunawa da Marigayi tsohon gwamnan jihar Katsina Umaru Musa Yar’adua.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami’an hulda da jama’a na hukumar jin dadin alhazan jihar ta Katsina, Alhaji Bello Badaru Karofi ya fitar daga can kasa mai tsarkin.

Alhaji Bello ya kara da cewa “Yanzu haka kuma Alhazan jirgi na biyu Sun kammala dawafin bankwanan su Cikin daren nan za’a daukosu zuwa filin sauka da tashi na jidda domin dawowarsu gida muna fatan suma Allah ya maidosu gidajensu lafiya.”

Mai karatu dai zai iya tuna cewa alhazai daga jihar ta Katsina sama da dubu biyu ne suka sauke faralin zuwa aikin hajji a wannan shekarar.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *