Wani yaro ya harbe yayar sa har lahira da bindiga a karamar hukumar Sandamu

Wani yaro ya harbe yayar sa har lahira da bindiga a karamar hukumar Sandamu

Daukar Nauyi: Rt. Hon. Abubakar Yahya Kusada

DAUKAR NAUYI: Hon. Salisu Yusuf Majigiri

Wani yaro ya harbe yayar sa har lahira da bindiga a karamar hukumar Sandamu

0
0

Wani yaro ya harbe yayar sa har lahira da bindiga a karamar hukumar Sandamu 

A jiya da yamma wani yaro dan kasa da shekaru 15 ya harbi yayarsa da bindiga har lahira.

Lamarin ya afku a kauyen Lugga Tori dake karamar hukumar Sandamu, in da matar take aure, matar sunan ta Hajara Sule tana aure a garin, sai wani kanenta yazo mata ziyara daga garinsu, da zuwan yaron bayan wani lokaci, Yaron ya hangi Bindiga irin ta maharba ajiye a gidan, kasancewar shi mijin maharbi ne, Yaron ya dauki bindigar ba tare da sanin illarta ba, ya saita wannan matar a daidai lokacinda ta dauko buta zatayi alwalar sallah ya danna kunamar bindigar inda ta sami matar a cikinta, saitin mararta. Nan da nan matar tace ga garinku nan.

Matar dai shekararta guda da aure bata da yaya.

Rundunar Yan sanda reshen karamar hukumar Sandamu sun kamo Yaron da kuma mijin matar domin bincike, bayan nan sun tura su State CID domin cigaba da bincike.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *