An kashe mutane da dama a wata arangama tsakanin makiyaya da manoma a Safana

An kashe mutane da dama a wata arangama tsakanin makiyaya da manoma a Safana

An kashe mutane da dama a wata arangama tsakanin makiyaya da manoma a Safana

0
0

yi asarar rayuka da dama a wata arangama da aka tsakanin filani making da kuma manoma a garin Gora na karamar hukumar Safana, jihar Katsina, kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya rawaito.

“Fadan ya afku ne bayan da wasu Fulani makiyaya suka shiga gonar wani manomi yana roron wake a gonarsa” inji Gambo Isa mai magana da yawun Yan sandan jihar Katsina a hirarsu da NAN.

Haka wata majiyar ta shedawa NAN cewa makiyayan sune suka fara kashe manomin a gonarsa a marecen ranar Talata.

Inda su kuma mutanen gari suka far wa makiyayan shima suma kashe shi .

Dare na yi sai dumbin yan uwan makiyayan suka shigo suna kururuwa domin daukar fansa, wnada hakan ya ja rasuwar mutum 12 da jikkata wasu 9.

Sai dai Mai magana da yawun Yan sandan jihar Gambo Isa ya ce tuni aka baza jami’an kwantar da tarzoma a yankin domin tabbar da kyakkyawan tsaro

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *