Hajjin bana: Gwamnatin jihar Katsina ta kayyade Naira 300,000 a matsayin kudin ajiya

Hajjin bana: Gwamnatin jihar Katsina ta kayyade Naira 300,000 a matsayin kudin ajiya

Hajjin bana: Gwamnatin jihar Katsina ta kayyade Naira 300,000 a matsayin kudin ajiya

0
0

Hajjin bana: Gwamnatin jihar Katsina ta kayyade Naira 300,000 a matsayin kudin ajiya 

Maigirma gwamnan jihar katsina Rt Hon Aminu Bello Masari Dallatun katsina matawallen Hausa ya Amince da Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar katsina da ta fara karbar kudin Ajiya ga masu niyyar zuwa aikin Hajjin dubu biyu da sha Tara (2019 Hajj) tun daga naira Dubu Dari ukku zuwa abinda ya wuce haka daga wannan watan Nuwamba (2018) har zuwa Maris na sabuwar shekara (2019) kamar yanda Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta umarci jihohi.

Ana Bukatar kowane maniyyacin aikin Hajjin na 2019 Hajj da su ziyarci ofisoshin Hukumar dake shiyyoyinta kamar haka Daura, Katsina, Kankia, Dutsin-ma da kuma Malumfashi domin bude Asusun Ajiyarsu tare da fara biyan kudin kujerar su tundaga wannan watan da Muke ciki.

Saboda haka Hukumar na shaida masu cewa ana bukatar maniyyaci daya ziyarci ofisoshinta na shiyyar da ya fito da Takardar shaida ta banki watau bank drapt,Hotuna guda sha biyu,Takardar shaida ta karamar Hukumar,Takardar shaida ta muharrami da kuma Wanda zaya tsaya ma maniyyaci watau grantor.

Daga karshe Hukumar na gargadi ga kowane maniyyaci ya tabbatar ya biya kudin shi ta hangar Takardar ta shaida biya ta banking ba tsabar kudi ake karba ba,kuma suyi Hulda kai tsaye da jami’anta dake ofisoshinta na shiyya guda bakwai dake fadin jahar nan.

Allah ya bada ikon yin hakan ameen sanarwa daga Badaru Bello Karofi Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar jin dadin Alhazai ta jihad Katsina.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *