Sunayen mutum 5 da ka iya zama Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Katsina

Sunayen mutum 5 da ka iya zama Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Katsina

Sunayen mutum 5 da ka iya zama Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Katsina

0
0

Daga, Ibrahm M Bawa

 

A yanzun haka ana zaman dakon jiran ganin wanda zai zama sabon Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina.

Hakan ya zama dole kasantuwar wanda ke shugabancin majalissar Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada ya lashe zaben cike gurbi na dan majalissar wakila na mazabar Kankiya, Ingawa da Kusada.

Sai dai gaba daya ana sa ran sabon Kakakin majalissar zai fito ne daga shiyar Daura, inda dama can ne wanda zai bar kujerar ya fito, ganin cewa shiyar Daura ita ke rike da kujerar ta Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina ta la’akari da yadda kowace shiya ta Katsina ake bata babban kaso wajen raba manyan mukaman jihar, tsakanin Gwamna da Mataimakinsa da kuma Kakakin majalissa.

Daga cikin wadanda ake sa ran za su gaji kujerar akwai;

1. Hon. Nasir Yahaya (Daura)

Hon. Nasir Yahaya mai wakiltar karamar hukumar Daura a majalissar dokokin jihar Katsina, shima yana kan gaba-gaba wajen wadanda ake hasashen cewa zai iya zama sabon angon kujerar, sai dai ana ganin ya yadda ya fito gari daya da shugaban kasa, hakan na iya zama kalubale a gare shi.

2. Hon. Tasi’u Musa (Zango)

Hon. Tasi’u Musa dan majalissar dokokin jihar Katsina ne dake wakiltar karamar hukumar Zango, ana hasken cewa yan majalissar za su iya mara masa baya, ganin cewa kusan ya fi sauran yan majalissar shekaru a cikin majalissar, sannan kuma ganin wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwani na takarar Sanatan shiryar Daura a jamiyyar APC Hon. Nasir Zangon Daura, suna a mazaba daya ne ta Zango/Baure, ana kuma ganin ko don wannan ana iya yi masu sakayya da wannan kujerar ta Kakakin majalissa.

3. Surajo Sani Manzo (Sandamu)

Surajo Sani Manzo dake wakiltar karamar hukumar Sandamu a majalissar dokokin jihar ta Katsina, an rawaito cewa shima yana yawancin kujerar Kakakin majalissa.

4. Hon. Sani Lawal (Baure)

Hon. Sani Lwal dake wakiltar karamar hukumar Baure, shima yana cikin na gaba-gaba da ake ganin zai iya samun kujerar, ganin cewa shima ya fito a shiyar Zango/Baure da tuni aka fara sakin jita-jitar cewa daga wannan shiyar ne za a fitar da sabon Kakakin majalissar.

5. Rt. Hon. Aliyu Sabi’u Muduru (Mani)

Rt. Hon. Aliyu Sabiu Ibrahim Muduru dan majalissar dake wakiltar karamar hukumar Mani, shima ana hasashen cewa zai maye gurbin shugabancin Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina, bisa lura da cewa shi ne Kakakin majalissar na farko tun bayan kamun ludayin mulkin APC a jihar Katsina.

Bayyana ra’ayinka a kan wanda kake son ya zama sabon angon kujerar Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina?

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *