Yadda gobara ta lashe kusan shaguna 100 a bakin General Hospital Funtua

Yadda gobara ta lashe kusan shaguna 100 a bakin General Hospital Funtua

Yadda gobara ta lashe kusan shaguna 100 a bakin General Hospital Funtua

0
0

Bayanan da suke fitowa daga garin Funtuwa cibiyar Kasuwanci da Noma na Jihar Katsina na cewa kalla Kusan rumfunan kasuwar da ke bakin asibitin Funtuwa ne suka Kone.

Wata majiyar da muka tuntuba da suka Hadar da masu rumfuna a wannan Kasuwa ta bakin asibitin Funtuwa ta tabbatar mana da wannan bayanin.

Gobarar dai ta tashi ne da Daren ranar Alhamis dinan 22/11/2018 dalilin da ake dangantawa da wuta ce da ta taso daga wurin masu girkin abinci da ke kasuwar bayan yan Kasuwa akasarin su sun tashi sun rufe shagunansu sun tafi gida.

Kamar dai yadda yan kasuwar suka shaida wa wakilinmu cewa wasu sun samu sun cire kayansu wadansu kuma kayan sun Kone kurmus.

Da wakilinmu ya tuntubi wani daga cikin manyan jami’an karamar hukumar ya shaida mana cewa ba zai ce komai ba a yanzu Sai dai kawai ayi addu’a domin Gobarar ta yi barna matuka

Da wakilinmu ya yi kokarin Jin ta bakin shugaban kwamitin rikon karamar hukumar wayar sa a Kashe take, Amma mataimakinsa ya shaida wa wakilinmu cewa a gaskiya a lokacin misalin karfe 10: 27 na dare yana kan hanyar kauyensu don haka Sai Gobe.

Total Views: 23 ,

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *