Abu namu: Mustapha Saddiq shugaban Katsina Post ya angwance

Abu namu: Mustapha Saddiq shugaban Katsina Post ya angwance

Abu namu: Mustapha Saddiq shugaban Katsina Post ya angwance

0
0

Daga, Ibrahim M Bawa

 

A yanzun nan aka kammala daurin auren shugaban kamfanin jaridar Katsina Post Mustapha Saddiq, mai samar da labaran Turanci da Hausa mu samman wadanda suke da alaka da jihar Katsina da kewaye a yanar gizo,
.
An daura auren Mustapha ne da amaryarsa Fatima Halliru Mainasara a Masallacin Tudu dake unguwar Abba Jaye cikin garin Dutsinma jihar Katsina.

Daurin auren ya sami halartar baki na jiki da wajen jihar Katsina, da kuma abokanan huldarsa ta kafafen sadarwar zamani.

Muna roko Allah Ya ta shi riko, wadanda ba su yi ba kuma Allah Ya basu ikon yi amin

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *