Tiryan-tiryan, yadda samarin Yawuri suka share kwanaki 105 suna kirgye buhun gyero

Tiryan-tiryan, yadda samarin Yawuri suka share kwanaki 105 suna kirgye buhun gyero

Tiryan-tiryan, yadda samarin Yawuri suka share kwanaki 105 suna kirgye buhun gyero

0
0

Daga, Ibrahm M Bawa

 

A yanzun haka matasan garin Yawuri ta jihar Kebbi, da suka tsunduma gardama a kan cewa yawan kwayoyin buhu guda na gyero sun dara yawan yan Nijeriya a yanzun sun sami sakamakon gardamarsu.

Matasan sun fara kirgar kwayar gyeron ne tun farkon watan Agastan da ya gabata zuwa yau Asabar da aka fitar da sakamakon kididdigar.

Mai magana da yawun kwamitin yan kidayar gyeron Ahmed Sarkin-Yaki ya bayyana cewa bayan kwashe kwanaki 105 ana kirge kwayar gyero dake cika buhu daya cur an gano cewa akwai kwayar gyero 11,979,868 Miliyan sha daya da dubu dari tara da saba’in da tara, da kuma dari takwas da sittin da takwas ne ke cikin buhun.

Daga karshe Sarkin Yaki ya bayyana cewa yawan mutanen Nigeria sun dara yawan kwayoyin gyero a cikin buhu daya.

Sai dai mutane da dama na ta kallon wannan aikin da matasan suka yi na kirgye buhun gyero a matsayin rashin aikin yi ne ya jawo masu haka.

A daya bangare kuwa an rawaito gwamnan jihar Atiku Bagudu yana cewa matasan ba sun yi wannan aikin bane domin rashin aikin yi a’a sun yi ne domin su caza kwakwalwarsu tare da yin wani bincike na musamman.

Daga karshe an yi kade-kade da bushe-bushe wajen bayar da kyauta ga wadanda suka lashe gasar a fadar Sarkin Yawurin

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *