An zabi Hon. Tasi’u Musa Maigari a matsayin sabon Kakakin majalissar Katsina

An zabi Hon. Tasi’u Musa Maigari a matsayin sabon Kakakin majalissar Katsina

An zabi Hon. Tasi’u Musa Maigari a matsayin sabon Kakakin majalissar Katsina

0
0

Daga, Ibrahm Bawa

 

 

A yanzun nan aka kammala zaben sabon Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina inda aka zabi Hon. Tasi’u Musa Maigari dake wakiltar karamar hukumar Zango a matsayin sabon Kakakin majalissar jihar.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan aje mukamin da tsohon Kakakin majalissar Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada yi ban kwana dajalissar a yau domin nasarar da ya samu ta lashe zaben cike gurbi na Dan Majalissar Kankiya, Kusada da Ingawa a majalissar tarayya.

Ko a kwanakin baya Katsina Post ta kawo maku sunayen wajen mutum goma dake zawarcin kujerar, inda ta bayyana cewa dama sabon Kakakin majalissar Hon. Zango shi ne kan gaba-gaba a wajen wadanda ake ganin za a zaba a matsayin sabon Kakakin majalissar.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *