Da Duminsa: Abubakar Yahya Kusada ya karbi rantsuwa a gaban Yakubu Dogara

Da Duminsa: Abubakar Yahya Kusada ya karbi rantsuwa a gaban Yakubu Dogara

Da Duminsa: Abubakar Yahya Kusada ya karbi rantsuwa a gaban Yakubu Dogara

0
0

Daga, Ibrahim M Bawa

 

A yau Laraba Kakakin majalissar wakilan tarayya Abuja Hon. Yakubu Dogara ya rantsar da sabbin yan majalissar wakilai guda uku da suka lashe zaben cike gurbi na yan majalissun dokokin tarayya da ya wakana a jihohi uku.

Tsohon Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada daga jihar Katsina, dake wakiltar kananan hukumomin Kankia, da Ingawa da kuma Kusada na cikin wadanda suka yi rantsuwar kama aiki a majalissar wakilan.

A kwai kuma na jihar Kwara da Bauchi dukkan su da suka lashe zaben cike gurbin a karkashin tutar jam’iyyar APC.

A kawun majalissar ne ya gabatar da sabbin zababbun yan majalissar, sannan Kakakin majalissar Dogara ya basu rantsuwa.

Bayan kammala rantsuwar ke da wuya suka yi musabahah da Kakakin majalissar da kuma shugaban masu rinjaye Mr Femi Gbajabiamila, da sauran takwarorinsu yan majalissar.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *