Yanzu siyasa ibada ce mai zaman kanta – Gwamna Masari

Yanzu siyasa ibada ce mai zaman kanta – Gwamna Masari

Yanzu siyasa ibada ce mai zaman kanta – Gwamna Masari

0
0

Yanzu siyasa ibada ce mai zaman kanta – Gwamna Masari 

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana shiga siyasa domin kawo cigaba ga al’umma a matsayin ibada da kowa ya kamata ya tsunduma ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wajen rufe wa’azin kasa da kungiyar Izalatil bidi’a wa’ikamatussunna ta gabatar a jihar Katsina.

Gwamnan ya bayyana cewa ya zama tilas ga dukkan yan kasa ciki kuwa hadda malaman addini da su shigo siyasa domin bayar da gudummuwar su.

Yace idan har aka bar siyasar ga wasu tsiraru da ake ganin kamar ba mutanen kirki ba  to fa lallai su din ne dai za su shugabanci al’umma baki daya.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *