Daman sai da na gaya maku APC wahala zata baku – Shema zuwa ga Katsinawa

Daman sai da na gaya maku APC wahala zata baku – Shema zuwa ga Katsinawa

Daman sai da na gaya maku APC wahala zata baku – Shema zuwa ga Katsinawa

0
0

Tsohon gwamna jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema ya bayyana cewa sai da ya yi hasashen mutanen jihar Katsina za su sha wahala idan suka zabi jam’iyyar APC sai kuma gashi yanzu suna yabawa aya zakinta, kamar dai yadda jaridar Leadership A Yau ta ruwaito.

Alhaji Ibrahim Shehe Shema ya fadi haka ne a lokacin bude yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar Katsina, inda ya bayyana cewa halin da mutane suka tsinci kansu ya isa misalin irin nasiha da kandakun da ya yi masu amma ba su ji ba.

Gwamna Shema wanda ya ce ya bar jihar Katsina ana biyawa yara kudin makaranta da kaisu karatu kasashen waje da bada magunguna ga masu juna biyu a asibiti kyauta amma acewarsa yanzu duk an bar wannan abin alheri kuma mutane suna ji kuma suna gani Kazalika ya bayyana cewa lokaci ya yi da jama’ar jihar Katsina za su yi karatun ta nutsu wajan ganin sun yi waje rod da jam’iyyar APC a jihar Katsina domin abubuwan da aka bari su dawo su cigaba.

Haka kuma ya bayyana gwamnatin APC a matsayin gwamnatin yaudara wanda ya ce yakamarta ‘yan Najeriya su dawo rakiyarta tun kafin ranar zabe ta zo domin suna da damar canza wannan yanayin da ake ciki.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa yanzu ya ragewa mutanen jihar Katsina su tabbatar sun canza wannan gwamnati saboda ta kawo yinwa da talauci da fatara da rashin aiki yi ga jama’a

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *