An fitar da sunayen wadanda suka sami aikin S-power Graduate (Duba sunaye)

An fitar da sunayen wadanda suka sami aikin S-power Graduate (Duba sunaye)

An fitar da sunayen wadanda suka sami aikin S-power Graduate (Duba sunaye)

0
0

An fitar da sunayen wadanda suka sami aikin S-power Graduate

23 January 2019

Ibrahim M Bawa

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta fitar da sunayen wadanda suka sami nasarar tantancewa, a sabon daukar aikin malaman koyarwa a sakandare ga masu kwalin digiri karkashin shirin S-power

A cikin jerin yawan mutanen da suka sami nasara a kananan hukumomin jihar Katsina guda 34, karamar hukumar Sabuwa ita ce ta fi mafi karancin wadanda suka sami nasara da suke su 9 ne kacal sunayensu ya fito

Haka kuma karamar hukumar Katsina ita ce ta fi kowace karamar hukuma yawan wadanda sunayen su ya fito, da yawansu ya kai 661, karamar hukumar Funtua kuma tana da sunaye 213 da suka sami nasarar samun shirin S-power din.

Haka kuma karamar hukumar Faskari tana da yawan mutum 32, karamar hukumar Dandume 19, Safana mutum 31, Danmusa 31, da sauransu da dama.

Tun farko gwamna Masari ya dauki kusan yan S-power dubu biyar masu karatun NCE ko diploma a kan aikin koyarwa inda aka zuba su a makarantun Furamaren jihar Katsina ana biyansu dubu ashirin-ashirin duk wata

Shirin S-power na gwamnatin Aminu Bello Masari, koyi ne da shirin N-Power na gwamnatin tarayya, da aka kirkiro su domin ragye zaman banza da samar da aikin yi ga matasa.

Ku latsa wannan tsanwan rubutun domin ganin cikakken jerin sunayen: https://drive.google.com/file/d/169Gk8zk-pdX2zJVMnuCTqSyYNNYN3jML/view?usp=sharing

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *