Uku-cikin-daya: ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Barawo, Dan Fashi kuma Mai Satar Mutane a Katsina

Uku-cikin-daya: ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Barawo, Dan Fashi kuma Mai Satar Mutane a Katsina

Uku-cikin-daya: ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Barawo, Dan Fashi kuma Mai Satar Mutane a Katsina

0
0

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Kasurgumin Barawo Dan Fashi Da Makami Mai Satar Mutane

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani kasurgumin Dan Fashi da Makami wanda ake zarginsa da satar shanu, fashi da makami da kuma satar mutane don yin garkuwa da su don neman kudin fansa.

A ranar 01/02/2019 da misalin karfe biyar na yamma ta hanyar bayanan sirri, rundunar ta yi nasarar cafke wanda ake zargin mai suna Ibrahim Muwange, dan
kimanin shekaru talatin da biyar. Dan asalin garin Duffar Mato Malamai dake Karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

An dai yi nasarar kama shi ne a garin Dayi, cikin karamar hukumar Malumfashi duk a Jahar Katsina.

Dama dai yana cikin tsarin wadanda jami’an suke nema ruwa a jallo, inda ake zarginsa da satar shanu a wurare daban daban tare da satar mutane da fashi da makami.

Haka nan yana daga cikin wadanda suke addabar
kananan hukumomin Danmusa, Malumfashi, Safana da Batsari a jihar ta Katsina.

A yayin da jamia’n suke gudanar da bincike, sun gano bindiga kirar AK 47 mai dauke da lamba kamar haka- NH 9634 a wurin wanda ake zargin.

Haka kuma ya amsa duk laifukan da ake tuhumarsa
da su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda
ta jihar Katsina, Isah Gambo shine ya fitar da sanarwar ga manema labarai.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *