‘Yan shi’a sun ce a zabi Buhari da Masari a Katsina

‘Yan shi’a sun ce a zabi Buhari da Masari a Katsina

‘Yan shi’a sun ce a zabi Buhari da Masari a Katsina

0
0

Kungiyar , samarin yan shi’a reshen jihar Katsina wato ‘Shi’ite Youths Political Forum’ sun bayyana cewa a zaben dake tafe nan da kwanaki 8, shugaban kasa Buhari da gwamna Masari sune za su zaba a lokacin zaben.

Kungiyar yan shi’an ta bayyana haka ne a jiya lokacin da ta kai wa Sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa ziyara a ofishinsa, kamar yadda Vanguard News ta rawaito.

Shugaban kungiyar na reshen jihar Katsina Malam Aminu Ibrahim Bara’a, ya ce dalilinsu na tsayar da Buhari da Masari a matsayin yan takarar da za su zaba, shi ne saboda ayyukan da suka shinfida na ci gaban al’umma a cikin kasar nan.

Bara’a ya ci gaba da cewa duk wani nan kasa na gari ya san da irin abubuwan ci gaban kasa da shugaban kasa Buhari ya shinfida a cikin kasar nan.

Shima a nashi jawabin Sakataren gwamnatin Mustapha Inuwa ya ce gwamnatin Aminu Bello Masari da APC a bude take ga kowa da kowa, kuma a shirye take da ta dauki shawarar kowa domin ci gaban al’umma.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *