Yadda yan Nijeriya ke ta ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dage zabe

Yadda yan Nijeriya ke ta ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dage zabe

Yadda yan Nijeriya ke ta ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dage zabe

0
0

Ibrahim M Bawa

 

A yau Asabar 16 February 2019 ita ce ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ta sanya domin gudanar da babban zaben shugaban kasa dana yan majalissar tarayya da suka kunshi yan majalissar dattawa dana wakilan Nijeriya, amma hakan bai yiyyu ba sakamakon daga zaben da INEC ta yi a daren yau.

A jawabin da shugaban hukumar zaben Nijeriya Farfesa Muhamud Yakubu ya fitar na dage zaben, ya ce kasantuwar gaza kai wasu kayayyakin zabe a wasu wurare kan lokaci, hukumar ba za ta iya gudanar da zabe a yau Asabar ba, don haka INEC ta dage zaben zuwa ranar Asabar mai zuwa 23 February domin gudanar da zabubbukan da ya kamata a yi yau, na shugaban kasa dana yan majalissar tarayyar.

Haka kuma shima zaben gwamnoni da aka shirya za a yi a ranar Asabar 2 ga watan Mach yanzu an mayar da shi zuwa ranar 9 ga watan na Mach shima, karin sati daya kenan.

Sai dai abin da ya jawo cece-kuce dangane da dage zaben, shi ne yadda ma’aikatan wucin gadi da INEC ta dauka domin gudanar da zaben, da suka matasa masu yi wa kasa hidima da daliban jami’o’i, an rika an tura su bakin daga, wasunsu ma sun kwana a cikin motocin daukar kayan aikin wasu kuma a kujerun makarantun Furamaren da za su yi aikin zaben.

Kwasam wajen misalin karfe 2:43am shugaban hukumar zaben Nijeriya ya fitar da cewa babu wannan zabe sai a mako mai zuwa.

Ko kwamitin gudanar da kamfen shugaban kasa na jam’iyya mai mulki APC ta nuna rashin jin dadinta, da dage zaben da INEC din ta yi, inda ta ce hukumar zaben ta bata masu lokaci.

Haka kuma a bangaren jam’iyyar adawa ta PDP dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar, zargi babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC da yin katsalandan a hukumar zaben, da cewa da masaniyarsa hukumar zaben ta dage zaben yau din.

Wasu kuma masu kada kuru’a na ganin dagawar da hukumar zaben ta yi domin domin samun damar kai kayan zabe a ko’ina abu ne mai kyau, domin ganin kowa ya samu damar yin zabensa.

A kuma wani bangaren wasu na ganin gazawar hukumar zaben, musamman da ta tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya, zabe na nan daram za ta gudanar da shi a yau, wanda ta kara wa yan takara kwarin guiwar ci gaba da kamfen da kashe kudadensu domin ganin sun sami nasara, sai ga shi kwatsam bayan kowa ya gama shiryeshiryensa suka ce babu zabe a yau Asabar.

Tuni dai kasuwar jaridu ke ci gaba da ci a kasuwannin Nijeriya domin karanta yadda dage zaben ya wakana.

Ku a naku ra’ayin ya kuke kallon wannan dage zaben,

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *