Daga karshe: Yan takarar APC za a yi zabe da su a jihar Zamfara – INEC

Daga karshe: Yan takarar APC za a yi zabe da su a jihar Zamfara – INEC

Daga karshe: Yan takarar APC za a yi zabe da su a jihar Zamfara – INEC

0
0

 

Ibrahim M Bawa

Jumu’a 22 Feb. 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa za ta yi aiki da umurnin kotun daukaka kara dake zamanta a birnin tarayya Abuja da ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ta hana a saka yan takarar jam’iyyar APC a jihar Zamfara bisa gaza aiwatar da zaben fitar da gwani da hukumar zabe INEC ta bayar da adadin kwanakin kaidar da ya kamata a kammala shi.

A sanarwar da INEC din ya yi a shafinta na Twitter ta ce a yanzun yan takarar jam’iyyar APC tun daga matakin Gwamna da yan majalissar tarayya da kuma na jihohi za a kara da su a cikin zaben da za a fara gudanarwa daga gobe Asabar 23 ga watan February 2019

Sai dai hukumar zaben ba ta bayyana bangaren ko wadanne yan takarar ne za ta saka a cikin zaben ba, kasantuwar yadda yan bangaren Gwamnan jihar mai barin gado Abdulaziz Yari, da bangaren Sanata Kabiru Marafa kowa ke bayyana cewa yan takararsa ne ke kan kaida

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *