Arc. Kebram ya taya yan majalissar tarayyar da suka lashe zabe murna, tare jan hankali a gare su

Arc. Kebram ya taya yan majalissar tarayyar da suka lashe zabe murna, tare jan hankali a gare su

Arc. Kebram ya taya yan majalissar tarayyar da suka lashe zabe murna, tare jan hankali a gare su

0
0

Ibrahim M Bawa

 

Shugaban kungiyar Mano ta Nijeriya wanda a Turance ake kira da All Farmers Association of Nigeria (AFAN) kuma babban jigo a jamiyyar APC a tarayyar Nijeriya Arc. Kabir Ibrahim Faskari (Kebram) ya taya daukacin ilahirin yan majalissar tarayya na jihar Katsina da suka lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar 23 February 2019, murnar lashe zabe lafiya.

A sakon taya murnar da ya fitar Arc. Kebram ya ce:

“Ina mai farinciki taya murna ga yan majalissar tarayyar da aka zaba domin su wakilce mu, na tsawon shekaru hudu masu zuwa nan gaba.

“Zan kuma fadada wanda sakon fatan alherin da taya murna a gare ku, tare da baku shawarar cewa ku yi amfani da damar da kuka samu wajen aiwatar da muhimman ayyukan da za su bunkasa rayuwar al’ummarmu, domin ta haka ne zabe zai sake zuwa cikin sauki tare da tsafta nan gaba a cikin Nijeriya.

“Ina mai tabbatar maku cewa Shugaban Kasa Muhammad Buhari bai kashe komai ba na kashin kansa, ko ya rasa barci a kan wannan zaben tazarcen nasa ba.

“A don haka mu yi koyi da shi, idan muna son ci gaba da rike wadannan mukaman siyasar, a lokacin da shi ya gama lokacinsa.

Dole mu fara tunanin makomar jam’iyyar APC bayan kammala wa’adin shugaban kasa Buhari daga yanzun.

“Ina mai yi maku fatan Allah ya baku ikon kammala wa’adinku lafiya, Allah kuma Ya yi maku jagora” inji Arc. Kebram

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *