Buhari na dab da lashe zaben shugaban kasar Nijeriya karo na biyu

Buhari na dab da lashe zaben shugaban kasar Nijeriya karo na biyu

Buhari na dab da lashe zaben shugaban kasar Nijeriya karo na biyu

0
0

Daga, Ibrahim M Bawa

 

Shugaban kasar Nigeria kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Muhamud Buhari na kan gaba a yawan kuru’un da aka kada a zaben sama da wanda babban abokin hamayyarsa ya samu a zaben

Duk da yake a lokacin hada sakamakon zaben jiho 23 ne aka gabatar a wajen tattara sakamakon zabe na INEC dake Abuja, amma alkalumman sakamakon zaben da hukumar zabe INEC ta jihohi ta kammala na kananan hukumomi 33 ya nuna Buhari ne zai iya lashe zaben Nijeriya.

A kuru’un shugaban kasa Buhari ya sami

Buhari APC 13,563,977

Atiku of PDP 10,236,469

Sai dai a yawan jihohi atiku na gaba da kwara daya cikin 33 din, inda Buhari ya samu 16 Atiku kuma na da jiha 17 har da babban birnin tarayya Abuja.

Jihohi 16 da Buhari ya lashe sun hada da: Bauchi, Borno, Ekiti, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Osun da kuma Yobe.

A jihohi 17 da Atiku ya lashe sun hada da FCT Abuja, Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Benue, Ebonyi, Edo, Enugu, Imo, Ondo, Oyo, Plateau, Taraba, Bayelsa, Delta da kuma jihar Rivers.

Dukkanin sakamakon wadannan jihohin hukumar zabe INEC ta bayyana su, sai dai akwai wadanda ba su gabatar da nasu a dakin tattara sakamakon zabe da INEC ke yi a shalkwatarta Abuja ba

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *