Buhari na gaban Atiku da kuru’u 1,004011 a jihohi 17 da aka gabatar

Buhari na gaban Atiku da kuru’u 1,004011 a jihohi 17 da aka gabatar

Buhari na gaban Atiku da kuru’u 1,004011 a jihohi 17 da aka gabatar

0
0

 

Daga, Ibrahim M Bawa

Talata 26 February 2019

Shugaban Kasa Muhammad Buhari na jam’iyyar APC ya shiga gaban Atiku Abubakar na jamiyyar PDP da kuru’u, 1,004011, na sakamakon zaben shugaban kasa na jihohi 16 gami da babban birnin tarayya Abuja da aka bayyana a dakin tattara sakamakon zabe da INEC ta tanadar a Abuja.

An gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalissar tarayya ne a ranar Asabar 23 ga watan February 2019, a dukkanin jihohin Nijeriya 36 gami da babban birnin tarayya Abuja

Kawo yanzun shugaban kasa Buhari na jamiyyar APC na da kuru’u 6,153,880, shi kuma Atiku na jamiyyar PDP na da kuru’u 5,149,869.

Bayan dan hutun da aka je, ana tsammanin za a dawo ci gaba da tattara sakamakon zaben yanzun da karfe 3pm na rana

Kadan daga cikin jihohin da APC ta lashe cikin wadanda aka gabatar sun hada da: Kogi, Yobe, Gombe, Kwara Osun, Ekiti, Kaduna, Nasarawa da sauran su.

Ita kuma PDP ta lashe, Abuja, Ondo, Adamaw, Enugu, Ebonyi, Abiya da sauransu da dama.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *