Rundunar Sojin Najeriya ta soma sintirin ‘Ofireshin Harbin Kunama IV a Katsina

Rundunar Sojin Najeriya ta soma sintirin ‘Ofireshin Harbin Kunama IV a Katsina

Rundunar Sojin Najeriya ta soma sintirin ‘Ofireshin Harbin Kunama IV a Katsina

0
0

Rundunar Sojin Najeriya za ta soma sintirin ‘Ofireshin Harbin Kunama IV a Katsina

Rundinar sojin Nigeria ta kammala shiri zata kaddamar da wani gagarumin farautar barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga wadanda suka buya a dazukan jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sokoto.

Rundinar ta sojin Nigeria tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro za ta fara kaddamar da wannan gagarumin rawar daji daga gobe Litinin 1-4-2019 har zuwa ranar 30-4-2019

Rundinar sojin Nigeria tana sanar da al’umma na wadannan jihohi guda uku cewa kar su ji tsoro su firgita sakamakon amon sautin manyan makaman atilari da na amo wanda sojojin kundubala zasuyi amfani da shi a farautar ‘yan bindigar, anyi kyakkyawan shirin da ba za’a cutar da marassa laifi ba.

Wannan sanarwan ya fito ne daga Manjo CLEMENT K ABIADE mataimakin maimagana da yawun rundinar sojin Operation Harbin Kunama, kuma ya roki al’umma da su yada wannan sanarwan

Rundinar sojin Nigeria zata kaddamar da wannan gagarumin yaki a daidai lokacin da rayukan ‘yan Nigeria suke cigaba da salwanta a jihar Zamfara, domin kamar yadda jaridar Rariya suka ruwaito yau ma sai da wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka kashe kimanin mutane tara a kauyen Kursasa dake karamar hukumar Shinkafi a jahar Zamfara.

Muna fatan wannan mataki da rundinar sojin Nigeria ta dauka ya zama sanadin kawo karshen kisan rayuka da akeyi a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto Amin.

Datti

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *