Yan sanda a Katsina sun cafke masu kaiwa barayin mutane man fetur

Yan sanda a Katsina sun cafke masu kaiwa barayin mutane man fetur

Yan sanda a Katsina sun cafke masu kaiwa barayin mutane man fetur

0
0

Yan sanda a Katsina sun cafke masu kaiwa barayin mutane man fetur

Rundunar Yansanda Jahar Katsina Sunyi Nasarar Chafke wasu Bata Gari Masu Safarar Man Fetur ga Yantaadda

A wata Ganawa da Manema Labarai da Kakakin Rundunar Yansandan SP Isah Gambo Yayi a Yau din nan yace Rundunar ta Gayyachi Yan Jarida ne domin sanar dasu irin cigaban da ake samu ta bangaren tsaro a Jahar, Musamman Yaki da Rundunar takeyi da Yaki da Satar Shanu, Fashi da Makami tareda Satar Mutane domin neman kudin Fansa.

SP Isah yace Idan zaa Iya tunawa a Kokarin Gwamnatin Jahar na ganin anyi Maganin Yan Taada a Yankunan Kanan Hukumomin Goma Sha Daya da Rashin Tsaro yafi Addaba a Jahar, a Ranar 14th January, 2019, Gwamnatin Jahar Katsina ta fitar da wata Doka wadda ta hana saida Man Fetur a cikin Jaraku a Fadin wadannan kanan Hukumomin.

Sakamakon haka a Ranar 28/03/2019 da kuma Ranar 01/04/2019, Bisa bayanan Sirri da Hukumar ta samu Jami’an Hukumar sunyi wani samame a Kanan Hukumomin Batsari da Dutsinma dake jahar Katsina Inda sukayi Nasarar Damke wadanda ake Zargi da Safarar Man Fetur ga Yan Taadar masu Farautar Jamaa, wadanda aka kama din Sun kware wajen wannan Sana’a tasu.

Wadanda aka kama din Sun Hada da:

Zaharadeen Mas’udu, daga Unguwar Alkali Katsina

Ibrahim Khalid. Dan kimanin Shekara 28 Sabon Gida, Katsina

Najib Dayyabu, Dan Kimanin ahekara 17 Unguwar Sarki, Batsari, Katsina

 

Halliru Yarima Dan Kimanin shekara 30 Unguwar Yarima, Dutsinma Katsina

Cikin Abubuwan da aka kamasu dasu sune :

Jarkoki Talatin da Ukku (33) Dauke da Man Fetur.

Jarkoki Ashirin da Hudu (24) wadanda babu komai a ciki.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *