Ku sadu da Sabi’u Tunde – matashin mai kudi kuma babban makusancin shugaba Buhari

Ku sadu da Sabi’u Tunde – matashin mai kudi kuma babban makusancin shugaba Buhari

Ku sadu da Sabi’u Tunde – matashin mai kudi kuma babban makusancin shugaba Buhari

0
0

Sabi’u Tunde dai shine mai taimakawa shugaban kasar Najeriya na musamman a ofishin sa wanda za’a iya cewa dukkan wanda zai ga shugaban kasar to tabbas sai ya bi ta hannun sa.

Sabi’u Tunde dai sunan sa na gaskiya Sabi’u Yusuf kuma an ce ana ce masa Tunde ne saboda babban aminin shugaban kasa kuma mataimakin sa a lokacin mulkin sa na soja watau Marigayi Babatunde “Tunde” Abdulbaki Idiagbon a shekarar 1983 zuwa 1985.

Haka kuma shi Sabi’u Tunde an ce dan uwan shugaban kasar ne domin kuwa da ne ga kanwar kawun nan nasa Mamman Daura.

Ana dai cece-kuce kan ainihin shekarun sa a duniya amma dai zance mafi karfi shine da kadan ya haura shekara 30 a duniya.

Katsina Post dai ta samu cewa Sabi’u Tunde yayi makarantar Furamare din sa a makarantar Bayajidda dannan kuma yayi Sakandire din sa a kwalejin koyon malin ta dukkan su a garin Daura.

Haka ma kuma an ce yayi karatun digirin sa a jami’ar Bayero ta Kano sannan kuma yayi hidimar bautar kasar sa a garin Kaduna.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *