An kashe mutum 36 a wani artabu tsakanin yan ta’adda da ‘yan banga a kauyen Kankara

An kashe mutum 36 a wani artabu tsakanin yan ta’adda da ‘yan banga a kauyen Kankara

An kashe mutum 36 a wani artabu tsakanin yan ta’adda da ‘yan banga a kauyen Kankara

0
0

An kashe mutum 36 a wani artabu tsakanin yan ta’adda da ‘yan banga a kauyen Kankara

Daga Ibrahim M Bawa

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a kauyen Tsamiyar Jino dake cikin karamar hukumar Kankara a sakamakon, daukar fansa da wasu yan bindiga suka kawo wa kauyen.

Majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito cewa, yamutsin ya samo asali a lokacin da yan bangar garin suka kashe wani da ake zargin cewa yana cikin yan ta’adda da aka bayyana sunansa da ‘Baban Kusa’ da yan bargar suka kashe ranar Lahadi da Kasuwar garin ke ci.

A lokacin da labari ya ishe sauran abokan dan ta’addan da aka kashe a daji, sai suka yo samame suma shigo garin cikin dare suka kashe mutane da dama, domin su dauki fansar dan uwansu.

Wani ganau ya shedawa Daily Trust cewa yan bindigar sun kashe mutum 27 a Unguwar Rabo, da 8 a Unguwar Sarkin Aiki da kuma mutum 1 a Centre Na Ade.

Mai garin Tsamiyar Jino Jaafaru Bello Jino, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana kisan da aka yi wa yan garin nasa a matsayin babbar masifa.

Sai dai a lokacin hada labarin, da majiyarmu ta tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa ya sha alwashin karin haske game da lamarin ba da jimawa ba.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *