Cikin fushi: ‘Yan banga sama 500 sun shiga daji neman yan bindiga a Katsina

Cikin fushi: ‘Yan banga sama 500 sun shiga daji neman yan bindiga a Katsina

Cikin fushi: ‘Yan banga sama 500 sun shiga daji neman yan bindiga a Katsina

0
0

Daga Hk TV Katsina

Kimanin Yan Sakai Dari Biyar ne Suka Shiga Daji Domin Yin Gaba da Gaba da Yan Taadda

Akallah Mutum Dari Biyar ne Yan Sakai wadanda suka fito daga Yankunan Sabuwa, Faskari, Kankara da Birnin Gwari sukayi gangami tare da Shiga Daji domin Tunkarar Yan Taadda masu Garkuwa da kuma kashe Mutane a wannan Yankin.

Sai Dai Labarin da muke samu bayada dadin Ji domin Yan Taadar akalla sun kashe Mutane Sama da Sittin da Daya (61) daga yankin Sabuwa da Kankara.

Wani ganau yace a Yankin Sayau dake Dungun Mu’azu Sun Gano Gawawwakin Mutane akallah Ashirin da Daya yayinda Kimanin Mutane Goma Sha Biyar kuma Sun Bata baasan inda suke ba.

Yan Taadan Dai suna cigaba da Korar Mutane daga Garuruwansu kimanin Kauyuka Goma Sha Daya ne duk Sun gudu Sun bar garuruwan nasu sakamakon Taaddanchin wadannan Mutanen.

Jamaar Garin Dungun Muazu sunche Suna Zargin Jamian Tsaron Soja da kin daukar Matakin da yakamata wajen tunkarar wadannan Miyagun, sunche tsakanin wajen da Sojojin suke da inda Yan taaddan suke bai wuce kilo meter Biyu zuwa ukku ba amma idan Jamaar Sun kai masu koke tareda sanar dasu zuwan yan taadan basa zuwa ko kuma suche baa basu Umarni ba daga sama, hakan nan ne yayi sanadiyyar Alumma ta tari Aradu da ka domin Tunkarar wadannan Mutanen da kansu.

A wannan Artabun Dai Ana kiyasta cewa Jamaar Gari sunyi Saar Hallaka Hilanin kimanin su Arba’in, inda su kuma suka kashe Mutan gari yan sakai kimanin sittin da Daya a wannan Arangamar.

Kakakin Rundunar Yansandan Najeriya Yankin Jahar Katsina ya tabbatar da Arangamar Sai Dai ya musanta yawan wadanda suka Rasa Rayukan nasu a Artabun, ya kuma tabbatar da cewa an Tura Runduna ta Musamman a wannan yankin domin kulawa da yankin.

Mazauna wannan yankin sun tabbatar da zuwan Jamian tsaron tareda cewa suna nan a Garin Dandume sunata Harbe Harbe cikin Gari har yanzu basu kaiga shiga cikin Dajin ba Inda Yan taadan suke.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *