Da Ɗuminsa: Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kankara sun kashe mutum 10

Da Ɗuminsa: Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kankara sun kashe mutum 10

Da Ɗuminsa: Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kankara sun kashe mutum 10

0
0

Da Ɗuminsa: Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kankara sun kashe mutum 10

Daga Ibrahim M. Bawa

Wasu yan bindiga da har yanzun ba a iya gane ko suwaye ba, sun kai hari a kauyen Yar Santa Sherere dake cikin karamar hukumar Kankara jihar Katsina, inda suka hallaka akalla mutum 10 kawo yanzun.

Wani mazaunin garin da ya shedawa majiyarmu ta Daily Trust ya bayyana cewa maharan sun shigo garin suna harbe harbe, tare da kona shaguna da gidajen al’ummar garin a yammacin daren jiya Lahadi.

Shima mai unguwar kauyen Dikko Sherere, ya sheda wa majiyarmu tamu ta wayar tarho cewa “A yanzun haka ba mu ko iya fita mu yi wa wadanda aka kashe zana’ida saboda tsoron kar su dawo su mame mu.

” A yammacin jiya mutum 8 ne suka kashe mana, amma kawo yanzun daga cikin wadanda suka raunata biyu sun kara mutuwa da yawansu ya kai 10 kenan” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa a yanzun haka mata da kanana yara na ta yin hijira da kafafunsu suna ficewa garin domin tsira da ransu daga hannun yan ta’addan da suka matsa wa kauyukan nasu da yawan kai farmaki.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *