‘Yan Najeriya na kewar ‘Yar Adua, Shekaru 9 bayan rasuwar sa (Tarihi da gwagwarmaya)

‘Yan Najeriya na kewar ‘Yar Adua, Shekaru 9 bayan rasuwar sa (Tarihi da gwagwarmaya)

‘Yan Najeriya na kewar ‘Yar Adua, Shekaru 9 bayan rasuwar sa (Tarihi da gwagwarmaya)

0
0

Jimami: ‘Yan Najeriya na kewar ‘Yar Adua, Shekaru 9 bayan rasuwar sa 

An haifi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a garin Katsina.

Mahaifinsa tsohon ministan Legas ne a jamhuriya ta daya kuma matawallen Katsina, sarautar da marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya gada.

Ya shiga makarantar firamari ta Rafukka a shekarar 1958, kuma daga bisani aka mayar da shi makarantar firamari ta kwana da ke Dutsimma.

A shekarar 1965 zuwa 1969 ya yi kwalejin gwamnati ta Keffi.

Daga nan kuma ya tafi kwalejin Barewa, inda ya kammala a shekarar 1971.

Ya shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1972 zuwa 1975, inda ya yi karatun digirinsa na fannin ilimin koyarwa da na kimiyyar sinadirai.

A shekarar 1978 ne ya koma jami’ar Ahmadu Bellon domin yin digirinsa na biyu a fannin ilimin kimiyyar sinadaren.

Aikin farko da Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya fara shi ne na koyarwa a kwalejin Holy Trinity da ke Legas a shekarar 1975 zuwa 1976 kuma daga bisani ya koma koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Zaria a tsakanin shekarun 1976 zuwa 1979 ya kuma ci gaba da koyarwa a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Zariya har zuwa 1983.

Daga nan ya yi aiki a wurare daban daban.

A lokacin jamhuriya ta biyu ‘Yar Adua ya kasance dan jam’iyyar PRP yayin da a wannan lokacin mahaifinsa ne mataimakin shugaban jam’iyyar NPN na dan wani lokaci.

A lokacin da janar Ibrahim Babangida ke shirin maida mulki ga hannun farar hula, Umaru Musa ‘Yar Adua ya kasance daga cikin mutanen da suka kafa wata kungiya mai suna Peoples Front wadda wansa Janar Shehu Musa Yar Adua ya jagoranta, kuma ita ce ta rikide ta zama jam’iyyar SDP.

A shekarar 1991, Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar SDP inda ya sha kaye a hannun Sa’idu Barda na jam’iyyar NRC.

‘Yar Adua ya sake tsayawa takarar gwamnan jahar Katsina a shekarar 1999 karkashin tutar jam’iyyar PDP, inda ya yi nasara, an kuma sake zabar sa a shekara ta 2003.

Alhaji Umaru Musa Yar Ada ya kasance gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa, a wani matakin da wasu ke ganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

Rasuwar Marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua

Marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa, ya sha kai da komowa zuwa kasar Saudi Arabia domin neman lafiya wanda har a wannan lokacin hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.

A lokacin da ya rasu, tashar talabijin ta tarayya da ke kasar ce ta bayyana rasuwar shugaban a daren Talata 5 ga watan Mayu.

Bayanin rasuwar shugaban na Najeriya Umaru Musa Yar ‘Adua ya jefa kasar cikin wani hali na tunani game da salon da batun mulki da kuma harkokin siyasar kasar za su dauka.

A ranar 6 ga watan Mayun 2010 ne aka yi jana’izar tsohon shugaban a mahaifarsa da ke jihar Katsina inda jana’izar ta samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na Najeriya.

Marigayin ya rasu ya bar mace daya Hajiya Turai Yar Adua da ya’ya bakwai. biyar mata biyu maza.

Marigayi Umaru `Yar’adua shi ne shugaba na biyu da ya karbi ragamar mulkin kasar bayan komawarta ga turbar Demokradiyya a shekarar 1999.

Kuma ya karbi ragamar mulki ne daga hannun shugaba Olusegun Obasanjo bayan wani zabe mai cike da takaddama a shekara ta dubu biyu da bakwai.

Mulkin Shugaban

Bayan hawan shi kan karagar mulki, shugaban ya fito da sabon salon mulki inda ya fito da manufofi bakwai da ya ke gani zai yi amfani da su domin tsallakar da kasar zuwa ga tudun mun tsira.

Wadannan manufofi da aka yi wa lakabi da ”7 point agenda” a turance sun hada da :

1. Habaka wutar lantarki

2. Wadatar da kasa da abinci

3. Habaka arzikin kasa

4. Ingantan harkokin sufuri

5. Garanbawul kan yadda ake mallakar filaye

6. Samar da tsaro

7. Inganta Ilimi

Wadannan su ne abubuwan da shugaban ya sa a gaba a wancan lokaci, sai dai yana cikin gudanar da wadannan ayyuka rashin lafiya ta kama shi.

Me Jama’a ke cewa shekaru tara bayan rasuwarsa?

Jama’a da dama musamman a kafofin sada zumunta na ci gaba da ta’aziyyar rasuwar shugaban kusan shekaru 9 kenan bayan rasuwarsa.

Jama’a da dama a shafukan sada zumuntar na tunawa da shi kan wasu abubuwan alheri da ya shuka a lokacin mulkinsa da suka hada da rage kudin man fetur, karin albashi musamman ga ‘yan sanda.

Haka ma dai ana ci gaba da tunawa da shi wajen irin rawar da ya taka wajen ganin cewa an samu sulhu da tsagerun yankin Niger Delta a wancan lokaci inda ya samar masu da sana’o’i da tallafin karatu da dai sauransu.

Shi ma tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ba a bar shi a baya ba wajen tunawa da Marigayi ‘Yar’adua domin a shafinsa na Twitter ya tuna da irin ayyukan da ya gudanar na gina kasar a wancan lokaci.

An tsakuro daga BBC Hausa

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *