Tsugune bata kare ba: Kotu ta yi barazanar sawa a kamo Sanata Mandiya

Tsugune bata kare ba: Kotu ta yi barazanar sawa a kamo Sanata Mandiya

Tsugune bata kare ba: Kotu ta yi barazanar sawa a kamo Sanata Mandiya

0
0

Tsugune bata kare ba: Kotu ta yi barazanar sawa a kamo Sanata Mandiya

Alkalin wata kotun majistare dake zaman ta a garin Funtua ya yi barazanar sawa a kamo masa Sanatan dake wakiltar shiyyar karaduwa a majalisar dattawan Najeriya, Bello Mandiya.

Alkalin ya yi wannan barazanar ne a cewar sa idan har Sanatan bai mutunta sammacin gayyatar da kotun ke yi masa ba akan wata kara da aka shigar a gaban shi.

A kwanan baya dai wani ya shigar da kara a gaban kotun yana tuhumar Sanatan da karya dokar kasa.

Wanda ya shigar da karar ya ce Sanatan ya tafka laifi lokacin da yayi takarar kujerar Sanata alhali kuma yana aikin gwamnati bai ajiye mukaminsa na Shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Katsina ba.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *