Bello Mandiya :- Munason Federal University Of Agriculture A Funtua Ko A Malumfashi – Daga Abdul Danja

Bello Mandiya :- Munason Federal University Of Agriculture A Funtua Ko A Malumfashi – Daga Abdul Danja

Bello Mandiya :- Munason Federal University Of Agriculture A Funtua Ko A Malumfashi – Daga Abdul Danja

0
0

ROKON ALUMAR FUNTUA ZONE

Ahmad Babba Kaita Yazama Barazana ga Al’umar Mazabar Sanatan Katsina ta Kudu!
Bello Mandiya :- Munason Federal University Of Agriculture A Funtua Ko A Malumfashi 

Nayi Amfani da wanan kalmar ne bawai don wani Abu ba saidai don Karin Maganar nan na hausawa dasuke cewa a rabe da Guzuma a harbi karsana to anan Babba kaitane Karsane Mukuma Namu Sanatan Yazama Guzuma!

Wai akace wata Miyar saidai a Makwabta Mudai Kam Allah yajarabcemu nafarko tin kafin zuwan Babba Kaita a Matsayin Sanatan katsina ta Arewa Yan Funtua suketa fama da kalubale na ayyukan Gina aluma more expecially a bangaren dalibai da ilimi da Samar ma Matasa aikinyi lokacin Abu Ibrahim Yana Sanatan mu!

Kafin 2019 mukaita rubuce rubuce da Sauran Matasa Irina muna kalubalantar wakilcin Sanata Abu Ibrahim kwatsam sai Allah yasake jarabtarmu inji hausawa sukace Wai

GARA JIYA DA YAU

Domin munaji munagani nafarko bamuda wakilci Mai kyau! Dukda Sanatan mu Bello Mandiya Yana Daya daga Cikin sanatoci Wanda suka jagoranci yakin neman zaben takara Sanata Ahmad Lawan Matsayina Shugaban Majalissa dattawa wato (Senate President) Kuma yasamu Nasara dukda hakan a bazan Wai sakarai yacema Wawa wofi!

Domin kuwa wanan bai Amfani Alumar Katsina ta Kudu wato (Funtua Senatorial District) da komaiba, munaji muna Gani yadda Sauran sanatoci suke kankajere wajen samarma matasansu matsuguni da aikinyi a Gwamnatin Tarayya Amman mu ko oho ba a dadeba Sanatan yasamarma wani aiki daganan Funtua Zone akaita CeCe kuce Wanda su Yan Daura zone Yan Mazabar Babba Kaita sukaita Mana shagube dakuma kalubalantar shi Sanatan nasu cewa donmi zaisamarma Matasan Funtua Zone aiki!

Funtua Zone Allah ya jarabcemu domin anriga anbarmu abaya kwanan nan Sanatan da Sauran Wakilai na Mazabar Daura sukaita fafutuka Akan Samar da Kwalejin Kimiyya da fasaha a Daura wadda Yanzu Haka ta tabbata kwatsam jiya saiga Sanatan na Daura yayi rubutu a shafinsa na sada zumunta wato Facebook cewa

“Federal Polytechnic of science and Technology Daura ta tabbata sauran Federal college of Fire service Kankia loading!”

Wanan idan kakalli Mazabar Funtua Zone ta Sanata datakeda LGA 11 sai kayi kuka na bakinciki bayan Rashin samarma daliban mu schoolarship dakuma tallafin karatu da Rashin samarmasu aikinyi a guraben aiki saikaga kuma yanzun babu wata makaranta wacce take Mai bada Degree wacce zata taimaki Yankin a ilmance!

Maigirma Gwamna Jahar katsina Aminu Bello Masari Yakawo NATIONAL OPEN UNIVERSITY OF NIGERIA STUDY CENTER KAFUR, Amman dukda haka Yan Siyasar mu da Wakilanmu sunkasa gane yadda zasu kawo hanyar dazasu taimaki Matasan mu su Sami gurbin karatu a wanane jamia ta Kafur, Misali ita Open University samun Admission nata na gurbin Degree baya Bukatar jamb, ko ace antafi strike yayin aiki kakar yadda conventional University sukexuwa idan kafara saikaga Kama da Yan siyasar mu sunada dabara kamar irin shi Sanata Bello Mandiya sai yatallafi Matasa Masu karamin suyi karatu domin muyi Tsare da Sauran yankuna na Jahar katsina Amman abin Shiru kakeji hakan yasa bama kowabane yasan ankowa Study Center a Kafur!

Bakowabane yasan Degree awarding Insituation ce don haka Nan da shekaru masu dama matasanmu anata barin mu a Baya!

Duk wani maikishin Yankinsa zaiso yaga wakilinshi Yana wakiltarshi kamar yadda Sauran Wakilai suke Amman Kash saidai muyita kishi anamana kwalele da gwalo munata kwadayi Amman Wakilanmu Suna nuna halin ko inkula da bukatu Wayanda zasuzo su taimaki chigaban Yankin a siyasance!

Ilimi, aikinyi da Samar da sano’i shine Abu mafi kyau Wanda zaitaimaki Rayuwar aluma tarike kanta da kanta Yazama wajibi muyita fadakar da Wakilanmu da hankaltardasu abinda muke bukata Wanda zaitaimaki Matasa da Yankin Funtua Zone Baki daya

Lokaci Yayi da Sanatan mu Bello Mandiya da Sauran Wakilanmu na Funtua Zone a matakin Majalissar Wakilai ta Tarayya da Majalissar Dokoki ta jaha dasu tashi Tsaye domin muma mudage ayi Tsare damu a kokowar samarda Ilimi da aikinyi ga Matasa

Bello Mandiya da Rep’s namu munason muji kunyi maganar federal University of Agriculture Funtua kowa Yasan Yankin Funtua da noma da kiwo kusan a cikin Kashi 100% Kashi 99% na mutanenda suke LGA 11 a Funtua Zone manomane na Rani da damina, Matasan mu suna mallakar Milyoyin kudi a noman Rani akan tumatur da kabeji da Albasa da sauransu Matasan mu ba ragwagebane manomane Wayanda basa jiran Gwamnati ko aikin Gwamnati, idan kakalli ma’auni na Tattalin arizikin Jahar katsina kasuwannimu Suna Daya Daga cikin kasuwanni mafi rinyaje fitar da hatsi a Rani da damina shin miyasa Wakilanmu bazasu kokari wajen nemanmana University of Agriculture ba?

Mun chanchanta yanada kyau Wakilanmu suntashi domin irin abinda Babba Kaita yakema Daura Yazama izina garesu sunsani muma muna bukata Kuma muna kishin yazo garemu!

Wani zaice qila nayi Sauri ki banyi uzuri ba to ga amsa miyasa Sauran wajaje akeyi? Babu uzuri ga Shugaban da yaroki Aluma suzabeshi domin yarike Amanar su ko waklilcinsu Akwai Wakilai a matakin Majalissar Dokoki dasuke tabukawa irinsu babangida talau na Malumfashi/Kafur Allah Yabasu ikon Chigaba dayi Amman lallaikam muna Bukatar Federal University Of agriculture ko a Funtua ko Malumfashi!

Wasu zasuce ai ba’ayin Federal University 2 a Jaha Daya ko Degree awarding Insituation aaa ba gaskia bane anayi domin Wanan ta agriculture ce bangaren noma kadai.
Amb Abdulrahaman Haruna Danja
abduldanjah88@gmail.com
08067548735

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *