Hukuncin kotu: Ina da yakinin Gwamna Masari zai yi nasara ko ina aka je – Sabo Musa 

Hukuncin kotu: Ina da yakinin Gwamna Masari zai yi nasara ko ina aka je – Sabo Musa 

Hukuncin kotu: Ina da yakinin Gwamna Masari zai yi nasara ko ina aka je – Sabo Musa 

0
0

Hukuncin kotu: Ina da yakinin Gwamna Masari zai yi nasara ko ina aka je – Sabo Musa 

Daya daga cikin masu taimakawa Gwamnan jihar Katsina a harkokin gudanar da mulkin sa kuma masoyin gwamnan da jam’iyyar su ta APC, Alhaji Sabo Musa ya bayyana cewa yana da yakinin Gwamnan zai doke abokan adawar sa a dukkan matakan shari’ar da ke kasar nan.

Alhaji Sabo ya bayyanawa kafar labarai ta Katsina Post hakan ne a wata zantawa da yayi da ita bayan sanar da hukuncin kotun kararrakin zaben Gwamnan jihar Katsina a farkon makon nan.

A cewar sa “Abun dariya ne ma a ce wanda yayi aikin gwamnati na tsawon shekaru sannan yayi kwamishina, kafin daga bisani ya zama wakilin mazabar sa a majalisar tarayya har ma ya rike mukamin na hudu a Najeriya sannan ya mulki jiha na tsawon sama da shekaru hudu amma ace wai bai da cikakkun takardun kammala karatun sa.

“A iya sani na babu jihar da tayi sahihin zabe a shekarar 2019 kamar Katsina domin kuwa ba bu ko da ran dabba da aka rasa kuma Gwamnan Aminu Bello Masari ne ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.

“Tabbas wannan abun takaici ne kuma hakan na nufin tamkar wasa da hankalin dukkan al’ummar kasa ne”, a cewar sa.

Mai taimakawa Gwamnan ya kuma kara da cewa jam’iyyar ta PDP da dan takarar ta suna da damar su daukaka karar su amma yana da yakinin cewa ba za suyi nasara ba.

Haka zalika Alhaji Sabo kuma ya yi kira ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya rika saka baki a cikin harkokin siyasar cikin gida na jam’iyyar sa ba wai ya zura ido yana ganin wasu da ke takama da kusancin su gareshi suna son tarwatsa ta ba.

Daga karshe kuma sai ya shawarci magoya bayan jam’iyyar ta APC da kuma masoyan Gwamna Aminu Bello Masari da su cigaba da jajircewa akan abaun da suke da ammana da su.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *