Uwar Gidan Gwamna Masari ta hori matasa akan shaye-shaye

Uwar Gidan Gwamna Masari ta hori matasa akan shaye-shaye

Uwar Gidan Gwamna Masari ta hori matasa akan shaye-shaye

0
0

Uwargidan gwamnan jihar Katsina Hajia Dr Hadiza Aminu Bello Masari (Uwar Marayu) ta kaddamar da shirin horar da matasa maza da mata yadda zasu bayar da gudummuwa wajen yaki da shaye-shaye kwayoyi da safarar su.

Shiri ne da aka dauko mutane 3 daga kowace karamar hukuma dake yankin Funtua zone wanda za’ayi masu bita ta kwanaki 5.

Manufar wannan shiri shine yadda zasu koma a kananan hukumominsu su taimaka ma mutanen da ke fama da wannan matsalar ta shaye-shaye da kuma kokarin rage ta a cikin Al’umma.

Wannan shiri yana kokari ne ta yadda duk wanda yake fama da matsalar shaye-shaye acikin matasa a taimaka ma sa da shawarwari ta yadda zai daina tare da kokarin kyautata rayuwar sa.

Cibiyar kula da mata da kananan yara ta jihar Katsina (Center for the advancement of mothers and children in Katsina) ce ta dauki nauyin wannan aiki, kuma ana sa ran bayan an kammala za’a gina wurin da za’a rika bayar da shawarwari tare da kokarin daidaita ma masu wannan matsala sahu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *