DAUKI DORA A KUNGIYAR DIREBOBI RESHEN KARAMAR HUKUMAR BAKORI

DAUKI DORA A KUNGIYAR DIREBOBI RESHEN KARAMAR HUKUMAR BAKORI

DAUKI DORA A KUNGIYAR DIREBOBI RESHEN KARAMAR HUKUMAR BAKORI

0
0

(Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya haramta ma kanshi aikata zalunci, yayi umarni da muguji zalunci sannan ya horemu da yin adalci a tsakanin al’umma.

A tsarin kowacce kungiya tanada tsarin zaben shugabannin da zasu jagoranceta a kuma yadda za’a gudanar da ita qungiyar. Amma abin mamaki sai muka samu akasin haka a Kungiyar Direbobi ta kasa reshen karamar hukumar Bakori.

Wa’adin mulkin shugaban wannan a Kungiya a Bakori yazo karshe, amma maimakon abi tsarin da doka ta tanada wajen zaben wanda zai maye gurbinsa. Kwatsam sai shugaba mai barin gado tare da hadin gwiwar wasu daga cikin mukarrabanshi suka fidda sabon shugaba ba tare da sanin sauran mambobi kuma ba tare da bin tsarin da doka ta tanada ba. Haka zalika, shugaba mai barin gado ya nuna ma shugabancin jiha wanda yake so ya k’ak’aba ma amatsayin sabon shugaba.

Wannan yunkuri ya harzuka zuciyar mambobin wannan kungiya mai albarka bisa ga dalilai kamar haka:

1. Ba’abi tsarin da doka ta tanada ba wajen wajen zaben sabon shugaba sannan kuma babu masaniyar sauran mambobin wannan kungiya

2. Shugaban da ake so a dora ba halastaccen dan Kungiya bane, kuma bama direba bane.

3. Wanda ba Dan kungiya ba, bai cancanci ya zama shugabanta ba.

A bisa wadannan dalilai ne, mu y’ay’an wannan kungiya muke kalubalantar wannan kamar karya da dauki dora da ake so ayi mana. Mun rubuta takardar kokenmu kuma mun aika da ita, zuwa ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace. Mun kaima Maigirma Makaman Katsina kuka a matsayinshi na uban domin ya tsawatar, haka zalika mun kaima jami’an tsaron nasu kofin. Mun kaima shugabannin wannan kungiya a matakin karamar hukuma, shiyyar Funtua da kuma matakin jiha. Muna jira muga matakin da zasu dauka.

Indai adalci akeso ayi to dole sai anyi rushen wannan doki dora da akeso ayi mana; a kirawo zama na dukkanin mambobi domin tattauna wannan matsala da ta kunno kai take son raba kawunan ‘yay’an wannan kungiya mai albarka. Sannan a shirya yadda za’a zabi sabon shugaba Sannan a tabbatar anyi abinda doka ta tana da.

Wannan itace hanyar samun maslaha akan wannan matsalar kuma ita kadaice hanyar wanzuwar zaman lafiya da dorewar hadin kan wannan kungiya.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *