Nasarorin da Garkuwan Katsina Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada ya samu a shekarar sa ta daya (1) da kama aiki

Nasarorin da Garkuwan Katsina Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada ya samu a shekarar sa ta daya (1) da kama aiki

Nasarorin da Garkuwan Katsina Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada ya samu a shekarar sa ta daya (1) da kama aiki

0
0

MOVEMENT FOR THE ACTUALIZATION OF HON. ABUBAKAR YAHYA KUSADA DREAM (MAYKUD).

Nasarorin da Garkuwan Katsina Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada ya samu a shekarar sa ta daya (1) da kama aiki

Rt. Hon Abubakar Yahya Kusada shine dan majalissar dokoki mai wakiltar shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa a majalissar dokoki ta kasa bakidaya a babban birnin tarayyar Abuja, shine tsohon kakakin majalissar dokokin jihar Katsina, wanda a halin yanzu yake jagorantar kwamitin raba dai-dai na kasa watau Federal Character Commission ( FCC) sannan shi dan asalin karamar hukumar Kusada ne dake jihar Katsina.

Bincike ya nuna cewa a tarihin wannan shiyya ba’a taba samun dan majalissa gogagge, mai kwazo, mai kuwala da jama’arsa sannan kuma wanda yafi kowa jajircewa wajen taimakon al-ummar wannan yanki kamarsa ba tun da aka mulkin damokaradiyya. Nasarorin daya samu a shekararsa ta farko akan ragamar mulki za’a iya kallonsu ta fuskoki daban-daban kamar haka:

1. Ta Fuskar Habbaka Ilimi.

2. Ta Fannin Inganta Lafiyar Al-umma.

3. Ta Fannin Habaka Harkokin Noma.

4. Ta Fuskar Magance Zaman Kashe Wando Tsakanin Matasa.

5. Ta Fuskar Bada Tallafi Wa Al’umma Sakamakon Bullar Annobar Cutar Mashako Watau Korona Bairos (Covid-19)

6. Ta fuskar Ayyukan Raya Kasa Da Cigaban Jama’a.

7. Ta Fuskar Zaman Zauren Majalissar Dokoki Da Kuma Fannin Shugabancin Kwamiti Da Yake Jagoranta.

8.Ta Fuskar Cigaban Siyasa

* TA FUSKAR HABBAKA ILIMI

Rt Hon Abubakar yahya Kusada ya samu nasarori daban-daban wajen ganin ilimin yankinsa ya habaka. Nasarorin sune kamar haka:

a. Daukar nauyin gasar kacici-kacici wadda Engr Ibrahim Sani Muhammad Yandoma ya kirkiro sannan kuma aka wanzar a shafin sada zumunta na Facebuk a yanar gizo tare da taimakon Jazuli Sulaiman Wakai da Muhammad Aminu Bala Kankia a lokacin da aka saka dokar hana fita daga gidaje sakamakon bullar chutar mashako kafin watan Azumin Ramadana da kuma lokacin shi a fadin Jihar Katsina.

b. Daukar nauyin Karatun gaba da sakandare na dalibai biyu (2) da sukafi kowa halattar gasar tare da nuna kwazonsu a gasar. Daliban sun fito daga kananan hukumomonin Kankiya da Kusada sannan ya lashi takobin samarwa dalibin da yafito daga karamar hukumar Ingawa gurbin aiki kasancewarsa wanda ya kammala karatu.

c. Daukar nauyin bada horon ilimi ga dalibai masu sha’awar shiga makarantun gaba da sakandare a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

d. Samar da daruruwan fama-faman zana jarabawar share-fage (JAMB) don samun damar shiga makarantun gaba da sakandare ga daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu son shiga makarantun.

e. Daukar nauyin bayar da horon na’ura mai kwakwalwa ga daliban da zasu zana jarabawar share-fage (E-JAMB) don samun damar shiga makarantun gaba da sakandare.

f. Samar da fama-faman zana jarabawar share-fagen shiga makarantar koyon jinya dake birnin Katsina ga daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu sha’awar shiga.

g. Samar da fama-faman zana jarabawar share-fagen shiga makarantar koyon ungozanci dake karamar hukumar Malumfashi a cikin jihar Katsina ga daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu sha’awar shiga.

h. Samar da fama-faman shiga makarantar kimiyya da fasaha dake cikin birnin Katsina ga daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu sha’awar shiga.

I. Samar da gidajen kwanan dalibai na manyan makarantun gaba da sakandare a Kano, Katsina, Daura da Dutsin-ma don amfanin daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

j. Samar da fama-faman shiga makarantun sakandare na kimiyya da fasaha dake cikin wasu kananan hukumomin jihar Katsina ga daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu sha’awar shiga.

k. Bayar da tallafi ga daliban asalin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu karantar koyon likitanci, Injiniyanci da kamamantansu.

l. Samar da fama-faman shiga makarantar koyon sana’ar noma dake garin Kafin-soli ga daliban shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu sha’awar shiga.

m. Samar da filin gina makarantar firamare a kauyen Rurumah dake karamar hukumar Ingawa.

n. Bayar da tallafi ga daliban da suka nuna hazaka wajen gasar kaci-kaci da muhawara wanda akeyi a makarantun sakandaren shiyyar ilimi ta Kankiya.

o. Daukar nauyin horon na’ura mai kwakwalwa ga matasan shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa don sajewa da wannan zamani na kimiyya.

p. Samar da fama-faman zana jarabawar WAEC, NECO da NABTEB na karshen zangon karatun sakandare wanda ake gudanarwa a watan Nuwamba da Disamba ga matasan shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa musamman ga masu sha’awar shiga.

* TA FANNIN FUSKAR INGANTA LAFIYAR AL-UMMA

Rt Hon Abubakar yahya Kusada ya samu nasarori daban-daban wajen ganin fannin lafiyar yankinsa ta habaka. Nasarorin sune kamar haka:

a. Gyara dakin kwantar da maras sa lafiya manya na asibitin karamar hukumar Kusada.

b. Biyan kudin tiyata ga maras sa lafiya fiye da dari da casa’in da takwas (198) a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa tare da biyan magungunan da zasu sha.

c. Samar da magunguna ga maras sa lafiya sama da dubu daya da dari tara da harba’in da bakwai (1947) a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

* TA FANNIN HABAKA HARKOKIN NOMA

Rt Hon Abubakar yahya Kusada ya samu nasarori daban-daban wajen ganin ya habbaka harkar noma a yankin da yake wakilta. Nasarorin sune kamar haka:

a. Gina rijijoyin ban ruwa sama da dari uku (300) don ganin an bunkasa noman rani tare da samar da isassun amfanin gona a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

b. Samar da injinan ban ruwa ga manoman rani sama da dari biyu da saba’in da takwas (278) a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

*TA FUSKAR MAGANCE ZAMAN KASHE WANDO TSAKANIN MATASA.

Rt Hon Abubakar yahya Kusada ya samu nasarori daban-daban wajen ganin ya magance rashin aikin yi a yankin da yake wakilta. Nasarorin sune kamar haka:

a. Samar wa matasan shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa daruruwan guraben ayyuka a gwamnatin tarayya.

b. Samar da guraben ayyuka ga matasan shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa a gwamnatin jiha.

c. Samar da guraben ayyuka ga matasan kananan hukumomin Katsina, Funtuwa, Kaita, Matazu, Mani, Musawa, Jibiya, Dan Musa, Baure, Batagarawa da Malumfashi a jihar Katsina da kuma karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.

d. Daukar nauyin rajistar neman aikin kaki a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa ga matasa musamman ga masu sha’awar shiga.

e. Bayarcda tallafi ga mutane masu kananan sana’oi daban-daban ko kuma a kungiyance a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

f. Samar da kayayyakin sana’oi daban-daban sama da dari uku (300) don rabawa ga wanda suka halacci makarantar horon koyon sana’oi a kowace santa. Wadanda suka amfana da shirin an zakulosu daga kowace mazaba cikin mazabu 31 na shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa,l tare da basu horon a bangarorin sana’oin da suka fi kwarewa kamar; sana’ar wankin mota, walda , bachi, dinki, kafinta, nika, markade, gyaran salula, gyaran famfuna da dai sauransu. Kayayyakin koyon sana’ar da aka basu sun haka da:
i. Kekunan dinki
ii. Injinan markade da na nika
iii. Kayan koyon aikin kafinta
iv. Injinan wankin mota
v. Injinan walda
vi. Injinan buga iska
vii. Injinan tukin tunkuza
viii. Kayan koyon gyaran waya
ix. Injinan chasar hatsi
x. Kayan gyaran famfuna

g. Samar da kekunan guragu sama da guda tamanin (80) ga masu matsalar kafa a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa don ganin sun samu saukin zirga-zirga.

h. Daukar nauyin karatun marayu da dama a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

i. Bayar da tallafi ga wadanda iftila’i ya fada mawa kamar gobara, rushewar gida sanadiyyar ambaliyar ruwan sama da dai sauransu duk a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

j. Samar da lasifikoki, tabarmi, injinan harba ruwa ga masallatai daban-daban a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

k. Samar da mototoci guda uku (3), daya a kowace karamar hukumar da take wakilta do saukaka zirga-zirga tare da samar da ingantaccen tsaro.

* TA FUSKAR BADA TALLAFI GA AL’UMMA SAKAMAKON BULLAR ANNOBAR CUTAR MASHAKO WATAU KORONA BAIROS (COVID-19).

Rt Hon Abubakar Yahaya Kusada ya samu nasarori da dama lokacin da aka garkame kananan hukumoni biyu (2) wanda yake wakilta sakamakon bullar cutar mashako a jihar Katsina. Nasarorin sune kamar haka:

a. Bayar da tallafin kayan masarufi; katan dubu daya (1000) na taliya, buhu hamsin (50) na masara tare da buhu ashirin (20) ga al-ummar karamar hukumar Kankia don rage radadin kulle sakamakon ciwon bullar cutar korona bairos.

b. Bayar da tallafin kayan masarufi; katan dubu daya (1000) na taliya, buhu hamsin (50) na masara tare da buhu ashirin (20) ga al-ummar karamar hukumar Ingawa don rage radadin kulle sakamakon ciwon bullar cutar korona bairos.

c. Bayar da tallafin kayan masarufi ga iyalan wanda suka rasu cikin watan Ramadana musamman a lokacin da ake kulle sanadiyyar bullar korona bairos.

d. Bayar da tallafin kayan masarufi ga limamai cikin watan Ramadana musamman a lokacin da ake kulle sanadiyyar bullar korona bairos.

* TA FUSKAR AYYUKAN RAYA KASA DA CIGABAN JAMA’A.

Rt Hon Abubakar yahya Kusada ya samu nasarori daban-daban wajen ganin yankin da yake wakilta sun amfana da ayyukan raya kasa tare da cigaban al-umma. Nasarorin sune kamar haka:

a. Gyara rijiyoyi da dama a wurare daban-daban don tabbatar da samun ingantaccen ruwan sha a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa. Misali, rijiyar unguwar Bakin Kasuwa dake mazabar Galadima ‘A a garin Kankiya, rijiyar kauyen Zamfarawar Doka dake mazabar Tafashiya a garin Kankiya da dai sauransu.

b. Gyara famfunan tuka-tuka na hannu sama da dari biyu da talatin (230) don ganin an samu ingantaccen ruwan sha a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa.

c. Gina sabbin rijiyoyi da dama masu amfani da hasken rana ko wutar lantarki tare da famfunan tuka-tuka na hannu a fadin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa don ganin an samu ingantaccen ruwa sha.

* TA FUSKAR ZAMAN ZAUREN MAJALISSAR DOKOKI DA KUMA FANNIN SHUGABANCIN KWAMITI DA YAKE JAGORANTA.

Rt Hon Abubakar yahya Kusada ya samu nasarori daban-daban a fannin zaman zauren majalissa da kuma bangaren shugabancin kwamitin da yake jagoranta. Nasarorin sune kamar haka:

-BANGAREN ZAMAN ZAUREN MAJALISSA:

A wannan bangare, Rt Hon Abubakar Yahya Kusada ya samu nasarori kamar haka:

a. Kawo korafin wadanda gidajensu suka rushe sakamakon ambaliyar ruwa a shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa don ganin gwamnatin tarayya ta basu tallafi tare da bin kwaf-kwaf don tabbatar da hukumar kula da faruwar annoba watu NEMA su tallafawa wanda annobar ta shafa.

b. Baya da goyon bayansa ga duk wani kudiri da wani abokin zaman sa ya kawo gaban majalissa madamar kudirin zaya amfani yan kasa baki daya.

-BANGAREN SHUGABANCIN KWAMITI:

Kafin nadin Rt Hon Abubakar Yahaya Kusada a matsayin shugaban kwamitin rabaa dai-dai na kasa watau Federal Character Commission (FCC), kwamitin ya samu jagoranta daga kwamaradawa daban-daban amma a lokacin shi mai girma dan majalissar dokoki ta kasa Rt Hon Abubakar Yahya Kusada an samu cigaba sosai wajen tabbatar da anbi doka da oda wajen raba gurabun ayyukan yi da gwamnatin tarayya ke samar wa daga ma’aikatu daban-daban a sassan kasa baki daya.

Al-ummar kasa da dama sai a lokacin shi suka san da kwamitin raba dai-dai, suka san aikin da yake gudanar wa dadai sauransu. An ganshi a fai-fan bidiyo da dama a yanar gizo a lokacin da yake kalubalantar wasu shuwagabannin ma’aikatun gwamnatin tarayya da dama kan salon daukar aikin su. Misali, Ma’aikatar kula da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje watau NEPZA, jami’ar garin Jos dake jihar Filatau, ma,aikatar kula da harkokin shige da fice na ruwa ta kasa baki daya watau NIMASA da da dai sauransu. Nasarorin daya samu sune kamar haka:

a. Shirya zama tare da jagorantar tattaunawa tsakanin kwamitin raba dai-dai da ma’aikatun gwamnati da dama don tabbatar da walwala da jindadin ma’aikata, tattaunawa kan batun daukar ayyukan maye gurbi tare da daukar sababbin ma’aikata.

b. Halattar tarukan karawa juna sani sama da hamsin a biranen Akwa-ibom, Legas da birnin tarayya Abuja.

c. Nasarar tabbbar da manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya sunyi sahihanci wajen daukar sababbin ma’aikata kamar; NNPC da dai sauransu.

d. Tabbatar da cewa duk ma’aikatun gwamnatin tarayya sun bi dokokin ma’aikatar da take kula da raba dai-dai na ayyukan da gwamnatin tarayya take samar wa a kowace ma’aikatar ta.

e. Tabbatar da cewa babu wani bangaren kasa da aka cuta wajen rabon guraban ayyukan da ma’aikatun gwamnatin tarayya ke samarwa.

f. Tabbatar da cewa duk wata ma’aikatar gwamnatin tarayya mai bayar da albashi mafi tsoka basu raba wa ‘yayan masu hannu da shuni guraben ayyukan da suke samarwa don ganin yaran talakawa suma sun amfana.

* TA FUSKAR CIGABAN SIYASA.

Kafin Garkuwan Katsina Rt Hon Abubakar Yahya Kusada ya zama wakilin shiyyar Kankiya, Kusada da Ingawa, manyan ‘yan siyasar wannan shiyya sun yarda cewa sara-suka, dabanci, kauranci, tara ‘yan iska, satar akwatin zabe da siyen ra’ayin masu zabe kadai ne hanyar samun mulki. Bayan Rt Hon Abubakar Yahya Kusada ya kasance mai wakiltar wannan shiyya sai ya lura cewa irin waccen siyasa bata dace da wannan shiyya ba, sai yayi bincike ya gano cewa ashe rashin aikin yi ne yake addabar matasan da suke bin ‘yan siyasar wancan lokacin.

Haka zalika, ya gano cewa cikin wadancan matasan da suke bin ‘yan siyasa akwai masu karatu da kuma wadanda suka iya sana’ar hannu. Wannan ne yasa yaga shi yaba bukatar irin waccen siyasar ta ba matasa kudi don siyen shaye-shaye da makamantansu, sai yanke shawarori kamar haka:

1. Samawa wadanda sukayi karatu ayyukan yi cikin wadannan matasa masu bin ‘yan siyasa don su dogara da kansu.

2. Samawa wadanda suka iya sana’ar hannu kayayyakin sana’oi’in ga wadanda ba suyi karatu ba cikin su don suma su dogara da kansu.

3. Daukar nauyin horar da wadanda ba suyi karatu ba, basu da wata sana’a da sukeyi sannan kuma basu iya wata sana’ar hannu ba daga bisani sai a basu kayayyakin da zasu taimaka masu wajen gudanar da sana’ar da suka koya don aiwatar da ita a zahiran ce.

Rt Hon Abubakar Yahya Kusada ya yarda da cewa ta wannan hanyar kadai ce da zaya yi magance zaman banzan wadancan matasa masu bin ‘yan siyasa don samun kudin shaye-shaye tare da rage cigaban yaduwar kauranci da sara-suka a siyasa.

Ubangiji Allah ya kara tsare mana Garkuwan Katsina Rt Hon Abubakar Yahya Kusada tare da bashi ikon ganin ya wanzar da duk wasu kudirorinsa na alkhairi ga wannan shiyya ta Kankiya, Kusada da Ingawa. Ameen

Daga:

Sakataren Kungiyar MAYKUD
Muhammad Aminu Bala Kankia

A madadin;

Rt Hon Abubakar Yahya Kusada
Dan majalissar dokoki ta kasa,

Daukacin Mambobi na Kungiyar MAYKUD

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *