Home Correspondent

Correspondent

Da na kammala wa’adin mulkina na 2 Daura zan dawo da zama – Buhari

  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin komawa Daura, bayan kammala mulkinsa na biyu. Buhari ya ce zai koma da zama a gidansa da zaran y agama mulkinsa. Ya bayyana akan ne a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya karkashin jagorancin Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a fadar Shugaban kasa […]

NYSC ta fara rijistar masu yi wa kasa hidima na rukunin A 2019

Ibrahim M Bawa   Hukumar matasa masu yi wa kasa hidima ta Nigeria NYSC ta fara gudanar da rijistar sabbin masu yi wa kasa hidima na zongon 2019 rukunin A, daga yau Litinin 4 ga watan March zuwa ranar Talata 19 ga watan March 2019 Bayanin haka na kunshe a cikin sanarwar da hukumar ta […]

Taya Murna: Arc. Kebram ya roki yan Nijeriya da su taimaki Buhari wajen ciyar da Nijeriya zuwa mataki na gaba (Next Level)

Arc. Kebram ya taya shugaban kasa Buhari murnar lashe zabe   Ibrahim M Bawa Shugaban kungiyar manoman Nijeriya (President Of All Farmers Association of Nigeria AFAN) Arc Kabir Ibrahim Faskari Kebram kuma jigo a jamiyyar APC, ya bayyana farincikinsa tare da taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben shugaban kasar Nijeriya karo na […]

Daga Karshe: INEC ta bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019

Daga, Ibrahim M Bawa Laraba 27 February 2019   Shugaban Kasa Buhari, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a wannan zaben 2019 da aka gudanar a ranar Asabar 23 February, ya kayar da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar Shugaban hukumar zaben Nijeriya Farfesa Muhamud Yakubu ne ya bayyana sakamakon zaben […]

Buhari na dab da lashe zaben shugaban kasar Nijeriya karo na biyu

Daga, Ibrahim M Bawa   Shugaban kasar Nigeria kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Muhamud Buhari na kan gaba a yawan kuru’un da aka kada a zaben sama da wanda babban abokin hamayyarsa ya samu a zaben Duk da yake a lokacin hada sakamakon zaben jiho 23 ne aka gabatar a wajen tattara […]

Buhari na gaban Atiku da kuru’u 1,004011 a jihohi 17 da aka gabatar

  Daga, Ibrahim M Bawa Talata 26 February 2019 Shugaban Kasa Muhammad Buhari na jam’iyyar APC ya shiga gaban Atiku Abubakar na jamiyyar PDP da kuru’u, 1,004011, na sakamakon zaben shugaban kasa na jihohi 16 gami da babban birnin tarayya Abuja da aka bayyana a dakin tattara sakamakon zabe da INEC ta tanadar a Abuja. […]

Arc. Kebram ya taya yan majalissar tarayyar da suka lashe zabe murna, tare jan hankali a gare su

Ibrahim M Bawa   Shugaban kungiyar Mano ta Nijeriya wanda a Turance ake kira da All Farmers Association of Nigeria (AFAN) kuma babban jigo a jamiyyar APC a tarayyar Nijeriya Arc. Kabir Ibrahim Faskari (Kebram) ya taya daukacin ilahirin yan majalissar tarayya na jihar Katsina da suka lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar 23 […]

Buhari ya ba Atiku kuru’u 500,000 a Katsina kawo yanzun a INEC

Ibrahim M Bawa Buhari na gaban Atiku da kusan kuru’u 500,000 da aka bayyana sakamakon su a jihar Katsina Kawo yanzun a yau Litinin a kananan hukumomi 20 cikin 34 dake cikin jihar Katsina, shugaban kasa Buhari na jamiyyar APC ya ba Atiku Abubakar na jamiyyar PDP tazarar sama da wajen kuru’u dubu dari biyar […]

Da Duminsa: jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin, Faskari, Batagarawa, Kaita, Jibiya da sauransu

Daga, ibrahim M Bawa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da sakamakon zaben karamar hukumar Faskari da aka yi na shugaban kasa da yan majalissar tarayya. Jam’iyyar APC mai mulki ita ce ta lashe zabubbukan gaba dayan su. A zaben shugaban kasa jamiyyar APC ta samu kuru’u44987, a inda mai bi […]

Daga karshe: Yan takarar APC za a yi zabe da su a jihar Zamfara – INEC

  Ibrahim M Bawa Jumu’a 22 Feb. 2019 Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa za ta yi aiki da umurnin kotun daukaka kara dake zamanta a birnin tarayya Abuja da ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ta hana a saka yan takarar jam’iyyar APC a jihar Zamfara bisa gaza […]